Najeriya za ta gudanar aikin Hajji 2026 a hukumance.
Kasar ta yi hakan ne sakamakon sa hannu a wata yarjejeniyar gudanar da aikin Hajjin da gwamnatin Saudiyya.
An yi bikin sa hannun ne a birnin Jeddah na Saudiya karshen mako.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar.
“Yarjejeniyar hujja ce cewa Najeriya ta shiga jerin ƙasashen da za su gudanar da aikin ibadar a bana”. In ji NAHCON
Sai dai babu tabbacin adadin maniyyatan da za su je aikin Hajjin kasancewar hukumomin Saudiyya sun rage yawan kujerun Hajjin na Najeriya daga 95,000 zuwa 66,000.
NAHCON ta ce, Saudiyya ta ɗauki matakin ne saboda Najeriya ba ta cike dukkan guraben da aka ware mata a bara ba, inda aka samu giɓin alhazai 35,872.
