
Sun zo Najeriya ne domin ya fi araha sosai a nan, kuma muna da kwarewa iri daya da ake da ita a ko ina a duniya.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a jawabinsa ga Kungiyar Kwararrun Likitocin Lafiyar Koda a wata ziyarar da suka kai masa a Abuja.
A cewar wata sanarwar da Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Watsa Labarai da Sadarwa, Stanley Nkwocha ya fitar.
“An samu sauyi a wajen zuwa neman lafiya a baya-bayan nan saboda irin kulawar da ake samu a wasu asibitocinmu.
“Kwanan nan majinyata 13 daga kasar Amurka suka zo Najeriya domin yin dashen Koda a Cibiyar Zenith Medical and Kidney Centre saboda ya fi araha sosai a nan, kuma suna da kwarewa iri daya da ake da ita a ko ina a duniya.”
A don haka akwai bukatar ci gaba da zuba-jari a fannin kwarewar ilimin likitanci don wannan abu ya dore”. In ji Kashim Shettima
Sanarwar ta kuma ce, Mataimakin Shugaban Kasa ya yaba wa Dakta. Olalekan Olatise, Babban Daraktan Kula Da Lafiya na Cibiyar Zenith bisa gudunmawar da yake bayarwa na kula da lafiyar koda, ya kuma bayyana shi a matsayin “mutum mai mutunci da kishin kasa” a kokarinsa na taimakon bil’adama.
Shettima ya kuma ce, ana samun karuwar masu zuwa Nijeriya neman lafiya ne daga kasashe ciki har da Amurka saboda kwarewa da kuma saukin da ake samu a fannin kiwon lafiya idan aka kwatanta da kasashen na nasu.
Sai dai ya nuna damuwa kan matsalar rashin kudi da kan tilasta wasu marasa lafiya a nan gida na sayar da muhallinsu da sauran kadarori don yi musu dashen ƙoda.
TRT ta rawaito cewa, Kungiyar Likitocin ta ziyarci Mataimakin Shugaban kasar ne gabanin babban taronta na Kimiyya Karo na 37 da za ta yi daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Fabrairu a Abuja, mai taken “Kawo Sauyi a Fannin Ciwon Koda a Nijeriya.”
.