Hukumar kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta zabi kamfanonin jiragen sama guda huɗu don aikin jigilar mahajjatan Najeriya na Hajjin 2025.
Kamfanonin da aka zaɓa su ne Air Peace Limited, Fly-Nas, Max Air, da UMZA Aviation Services Limited, bayan tantancewa daga cikin masu neman izini 11.
Kwamitin tantancewa mai mambobi 32, wanda ya haɗa da ƙwararrun masana jiragen sama da wakilan hukumomi kamar NCAA, FAAN, da ICPC, ya gudanar da aikin tantancewa tun watan Nuwamba 2024.
Haka nan kuma, an zaɓi kamfanonin jigilar kaya guda uku don ayyukan bana.Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya taya kamfanonin da suka yi nasara murna tare da jan hankalinsu kan cika alkawuran da suka ɗauka.
Har ila yau, ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikin Hajjin 2025 tare da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya a birnin Jeddah.
Taron sanya hannu ya samu halartar manyan jami’an Najeriya, ciki har da mambobin kwamitocin majalisa kan harkokin ƙasashen waje da jami’an Saudiyya daga ma’aikatar Hajji.
Wannan yarjejeniya ta tabbatar da shirin Najeriya na aikin Hajjin bana da tare da ƙarfafa dangantaka da kasar Saudiyya.