
NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar – don fara fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce an kayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alkalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.
Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Najeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yanda ta samu a bara.
Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Najeriya – inda ya ce ƙoƙari da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin saukaka musu.