
Gobarar ta faru ne a kauyen Zago, ta yini tana ci, ta kuma kone gidaje da dabbobi da kuma rumbunan abinci.
Wata gobara ta tashi a kauyen Zago da ke Karamar Hukumar Dambatta ta kuma mummunan ta’adi a kauyen, a inda ta kone gidaje da dabbobi da kuma rumbunan abinci.
Shaidun gani da ido sun ce, gobarar ta tashi ne a ranar Laraba.
Ta kuma tashi ne tun kimanin karfe 9 na safiyar Laraba kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4 na yamma.
Sakamakon wahalar da aka fuskanta wajen samun ruwa da kuma matsalar hanya da ta hana jami’an kashe gobara isa wurin da wuri.
Dagacin kauyen, Yunusa Isma’il ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da yin kira ga Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta kai dauki ga mutanen da gobarar ta shafa.
Gobarar ba a gano musabbabinta ba, kuma har yanzu ba a tantance yawan asarar da aka tafka ba sai dai ta kone gidaje da dabbobi da kuma rumbunan abinci.
Jama’ar kauyen na ci gaba da kokarin farfadowa daga wannan ibtila’i.
Advertisement