Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Abuja.
Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya ce rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake zargin masu ƙwacen fili ne suka je ƙauyen tare da ‘yan sanda daga ofishin Byazhin, suna ƙoƙarin ƙwace wani fili a ƙauyen.
Dangana, ya ce lokacin da mazauna ƙauyen suka gan su, sai suka taru suka toshe hanya don hana su zuwa wajen filin.
Ya ce mutanen ƙauyen suna riƙe da sanduna da duwatsu, inda suka fuskanci jami’an tsaro.
Daga nan ’yan sandan suka fara harba barkonon tsohuwa da harsasai.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke garin Bwari domin kula da su.
