Rahotanni sun bayyana cewa mutane uku sun jikkata yayin da wasu shaguna suka ƙone sakamakon tashin gobara a wata motar dakon Gas, a yankin Kwangila da ke Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.
Wannan na cikin sanarwar da hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta kasa reshen jihar Kaduna ta fitar ga manema labarai.
A cewar sa, Motar wadda ke ɗauke da iskar gas ta kama da wuta ne yayin da ta ke ajiye a gefen hanya a kan hanyar Funtua zuwa Zariya.
Sanarwar ta kuma ce gobarar ta shafi shagunan da ke kusa tare da jikkata mutane uku da aka kai asibiti domin samun kulawar likitoci.
Kazalika, sanarwar ta ce jami’an agajin gaggawa sun samu nasarar shawo kan gobarar tare da daƙile yaɗuwarta zuwa wasu wurare da ke maƙotaka da gurin.
Hukumar ta kuma buƙaci masu ababen hawa da su yi taka-tsantsan yayin wucewa yankin tare da bin umarnin jami’an tsaro, don gujewa abinda ka iya zuwa ya dawo.
