
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu.
Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitocin ƙwaƙwalwa ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana.
Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar.
Da yake bayani game da “Samar da kayan kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin yanayin agajin gaggawa,” Abayomi ya bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalolin ciwon taɓin hankali a tsakanin ‘yan Najeriya.
Da yake ambaton Ƙididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, masanin likitancin ya ce ɗaya daga cikin mutane takwas na fama da matsalar taɓin hankali.
Sai dai a Najeriya Abayomi ya ce adadin ya fi haka inda aka ƙiyasta kimanin ‘yan ƙasar miliyan 60 ne ke fama da matsalar taɓin hankali.
Kuma idan aka dubi adadin ƙidayar ’yan ƙasar zuwa miliyan 200 ko miliyan 240, wannan na nuna ɗaya cikin mutum biyar ko ɗaya cikin mutane shida da ke da rashin lafiyar tabin hankali.