Tsararrun da ya sake su 13 ana zargin su da aikata laifin fashi da makami, ya kuma aika hakan ne cikin maye.
Wannan lamari ya faru ne a birnin Lusaka ta kasar Zambiya a ranar Talata jajibirin Sabuwar Shekara.
Dansanda mai suna Titus Phiri, mai mukamin Sifeto, ya kwace makullin Sel din da ’yan fashin da suke kulle, ya kuma bude su sannan ya ce, duk su yi tafiyarsu.
Sauran abokan aikinsa na ofishinsu dake Leonard Cheelo na birnin Lusaka, sun numa matukar mamakinsu kan faruwar lamarin.
Rahotanni sun ce bayan tserewar tsarrarun da ake tuhuma da manyan laifuka, Sifeto Phiri shi ama yayi nasa wuri, ba san inda ya shiga ba.
Rahotani na cewa, daga baya Sifeon ya shiga hannu da kyar, yayin da aka shiga farautar masu laifin da ya sake.
Wata majiya ta ce Sifeton ya taba irin haka a shekarar 1997, inda wani ya ba da umarnin sakin wasu tsararru 53 ba tare an gurfanar da su agaban kotu ba.