Gwamnatin Kano ta yi kira ga jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu ba annoba ba ce, ta kuma dauki matakan dakile cutar
Kwamishinan Lafiya Dakta Labraran Ahmad Yusuf ne ya bayyana haka a cikin wata sanarawa da ya fitar kan lamarin a rana Talata.
Ya kuma ce, ma’aikatarasa ta yi tsaye kan lamarin ta na kuma daukan duk matakan da suka kamata na dakile yaduwar sa da kuma tasiri kafin ya zama wata barazana.
“ Za mu rika yin mitin duk sati na daukar matakin dakile wannan cuta. Kuma mun saka za a yi abin da ake cewa, Surveillance, kowacce Karamar Hukuma za a rika bibiya da kuma duddubawa tsakanin mutum da kuma dabbobi musamman masu kiwon wadanna tsuntsaye ana ganin me ke faruwa a gare su ana kuma aiko da rahoto kullum” inji shi.
Kwamishinan lafiyar ya bayyana alamomin cutar ga dan adama sun hada da zazzabi da fitar majina da jan ido da kuma sauransu.
Ya bukaci masu sana’ar sayar da kaji da su zama idon hukuma na farko a wurin lura da alamomin cutar a tsakanin tsuntsayen da kuma kai rahoto zuwa ga hukumomin da suka dace donm daukar mataki na gaggawa.