
Gamayyar Kungiyar Murya Daya Ta Matuka Baburan Adaidaita Sahu Ta Jihar Kano ta ce, za ta goyi bayan matakin gwamnati na shirin fara hukunta masu karya sabbin ka’idojin kula da fitulu da gwamnatin Kano ke ci gaba da sanyawa
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban gamayyar kungiyar, Nazifi BK gidan Kudi a hirarsa da Premier Radio a ranar Alhamis.
Shugaban ya ce, suna maraba da wannan mataki, sannan ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kano ta yi b duba na musamman gare su.
“ina kira da gwamnati ta yi duba na musamman ga masu tuka babur din adaidaita sahu na samman na horar da su irin sabbin ka’idojin kula da titununan.
“Sannan ina kira jan hankalin sauran matuka baburan adaidaita sahun da su ci gaba da bin doka da oda, a yunkurin inganta harkokin sufuri a fadin Kano da kewaye”. In ji shi.
A farkon makon nan ne Mai ba gwamnan Kano shawara kan harkokin sufiri Danladi Idris Karfi ya sanar da cewa, gwamnatin Kano ta fara yunkurin samar da kotunan tafi da gidanka domin hukunta mutanen da suke karya sabbin ka’idojin kula da hanyoyi, ciki har da dirobobin babur din adaidaita sahu.