Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tsaurara tsaro a kan iyakokin jihar bayan wani taron bitar dabarun yaki da ta’addanci.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a madadin Kwamishinan ‘yan sanda, ya ce CP Bakori ya yaba wa jami’an kan jajircewa da kuma hidimar da suke yi wa rundunar da kuma al’ummar jihar Kano.
Ƴan Sanda sun kama jami’an tsaro na bogi a Kano
Kwamishinan ‘Yansanda ya tsaurara bincike kan Mesar da ta kubuce a birnin Kano – Sarki Sunusi
Kwamishinan ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar.
CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda.
