
Daga Khalil Yaro
La’akari da yadda NAFDAC ta kama tarin magunguna jabu da ake sakewa mazubu da kwananan wata a jihar Abia
Wata kwararriya Mai Ilimin hada magunguna, Famasis Zulaihat Sani ce ta yi wannan kiran a hirarta da wakilinmu a ranar Lahadi.
Malama Zulaihat ta ja hankalin al’umma da su rinka lura sosai wajen sayen magani don gujewa jebun magani ko wanda aka sauyawa mazubi.
“Shan maganin da wa’adinsa ya kare na da illa mai hatsari wacce ka iya haifar da wani ciwon sabo ko kuma ta’azzara wanda mutum ke dauke da shi.
“Idan wa’adin magani ya kare babu wata hanya da ake bi domin ya amfanar da mutum, sannan kuma wajibi ne asibiti da wuraren da ake ta’ammali da magani da su ware inda da za a ajiye maganin da ya lalace,
Sannan duk ta ce, duk maganin da wa’adinsa ya kare to yana juyawa ne ya koma guba ko wani abu da kan iya cutar da jama’a, don haka ta yi kira ga hukuma ta dau mataki.
“Ina kuma kira ga hukumomi da su ci gaba da sanya ido domin dakile bazuwar jabun magunguna ko wadanda wa’adin su ya kare don kare lafiyar al’umma”. Inji ta.
A karshen makon da ya wuce ne jami’an Hukumar Kula da Ingancin Maguguna Da Abinci ta Kasa NAFDAC suka gano wani katafaren wuri da aka jibge magunguna jabu da sauyawa wadanda wa’adin aikin su ya kare mazubi a jihar Abia.