
Kungiyar musulmi masu da’awa wato Muslim Professionals in Da’awa (MPD) ta duba marasa lafiya da ba su magani kyauta fiye da 500 a nan Kano.
An gudanar da aikin ne ranar Asabar a masallacin Juma’a na garin Gundutse, dake Karfi ‘Yan Masara.
Da yake jawabi dagacin garin Gundutse, Ibrahim Ahmad, ya yabawa kungiyar bisa tallafin duba lafiya da bayar da magani kyauta da ta yiwa al’ummar garin.
A nasa bangaren shugaban kungiyar a nan Kano Sale Adamu Kwaru ya ce ba wannan ne karon farko da suke duba marasa lafiya da basu magani kyauta a sassafe daban daban na kasar nan ba.
Baya ga wadanda kungiyar ta Muslim Professionals in Da’awa ta duba tare sa basu magani an kuma ware wasu masu yanar ido da ciwon kaba inda za ayi musu aiki kyauta.