Daga : Nafiu Usman Rabiu
Malamin da fara tafsiri a taron jama’a Shiekh Tijjani Usman Zangon Bare bari ya rasu ne 25 ga Disambar 1970.
Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari shine malamin da ya fara tafsiri a bainar jama’a a kofar gidansa bayan ya samu izini daga Sheikh Ibrahim Inyas a shekarun 1950.
An rawaito cewa, a wata ziyara da shehun ya kai Kaulaha, ya ga Inyasa yana tafsiri a bainar jama’a, kuma a Kano duk da shaharar birnin a fagen ilimi da kuma yawan malamai ba a yi, sai dai a masallatai kuma tsakaninsu kadai.
“Ganin haka shehun malamin ya kafa nasa tafsirin a kofar gida a karon farko wanda ya zamo wani abu sabo a waccan lokacin da hakan ta sa mutane yin tururuwa don saurare”. A cewar Dakta Maude Gwadabe a shafinsa na Tuna Baya, a jaridar Aminiya.
Haka kuma shine mutum na farko ya fara yin taron mauludi a kofar gidansa bayan sallar magriba zuwa wayewar gari, bayan samun izini daga shehinsa a Kaulaha.
Haihuwarsa
Tarihi ya nuna an haifi shehun malamin a birnin Kano a farkon a shekarun 1914.
Mahaifinsa shine Malam Usmanu, Mahaifiyarsa kuwa malama Rabi.
Ya kuma fara karatun Alqur’ani Mai Girma da Littattafan Ilimi a wajan Baffansa Malam Rafa, ya kuma yi karatu wajen Shehu Salga da Shehu Sani Shatsari da kuma Shehu Abubakar Mijinyawa.
Shehun malamin gwarzon malami ne kuma halifa ne daga cikin halifofin shehu Ahmadu Tijjani, kuma yana daga cikin manyan almajiran shehu Ibrahim Inyass.
Hidimarsa ga Addini
Malamin ya bayar da gudummawa ga ilimi da kuma cigaban addinin musulunci ta fuskoki da dama.
Domin ya shiga cikin kauyuka yin wa’azi, sannan kuma shine mutum na farko da ya fara kafa makarantun Islamiyya ta dare don koyar da yara da kuma iyayen yaran addini.
A zamaninisa an samu malamai wadanda suke zuwa daukar tafsiri wajensa, wadanda wasunsu da yawa suma malamai ne, wasunsu ma sun haife shi.
Almajiransa
Daga cikin almajiran shehu da suka zama malamai akwai Mal. Abduwa da Mal. Mahmud Salga da Mal. Dan Almajiri da Mal. Sulaimanu Kila da Malam Isma’ila Ibrahim da Mal. Alin Alkali da sauransu.
Kowannansu a rayuwa sai da ya zama ba shi da sa a fannin Ilimi da kuma koyarwa.
Rasuwarsa
An rawaito cewa kwanaki kadan kafin mutuwarsa ya halarci wani majalisi a garin Bichi a inda ya yi wani tafsiri mai ratsa zuciya.
An kiyasta cewa shehun malamin ya rayu kimanin shekara 56 zuwa 57, ya kuma rasu a ranar Juma’a 27 ga Shawwal 1390 hijira wanda yai dai-dai da 25 ga watan Disambar 1970.
Sannan ya kuma bar ‘ya’ya 17 maza 4 da kuma mata 13