
Daga Mustafa Mohammed Kan Karofi
Ƙaramin Ministan gidaje Yusuf Abdullahi Ata ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Juma’a.
Ata ya ce, gwamnatin tarayya na Allah wadai da kalaman da mataimakin gwamnan kano yayi ga shugabar Tinubu.
A inda ya zargi shugaban da kitsa rikicin masarauta Kano tare da zaunar da sarki na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Sarki na Nassarawa da ya kira makabarta.
“Sha’ani na masarautar kano yana gaban kotu, don haka ya zama wajibi a yi biyayya da umarnin ta.
“Amma gwamnatin Kanon na neman bijire wa kotun wajen daukar nauyin wasu matasa domin su gudanar da zanga-zanga kan cewa sai sarkin Kano na sha biyar ya fita daga gidan Nassarawa.” In ji shi.
Karamin ministan ya kuma yi tir da tsarin mulkin gwamnatin Kano na yadda suke fitowa kafafen yaɗa labarai suna kalaman da basu dace ba ga jagororin ƙasar nan.