Mazauna yankin sabon gari sun nuna gamsuwa da yadda gwamnatin Kano bata manta da su ba, a ayyukan raya jihar Kano da take ci gaba da yi a sassa daban daban na jihar.
Shugaban majami’ar Iklisiya Wonders Gospel ministries anan Kano Reverand Zaphaniya Isa ne ya bayyana hakan yayin hira da manema, yana mai cewa ayyukan tituna da gwamna Abba Kabir Yusif ke yi a yankin sabon gari zai taimaka musu ta bangarorin da dama.
Reverand Zaphaniya Isa ya kara da kira ga gwamnan ya waiwayi titunan Sarkin yaki da kuma Gold Coast duba da halin da suke ciki.
Reverand Zaphaniya Isa ya bukaci yan siyasa su dinga koyi da magabata irin su marigayi Audu Bako wajen samar da ayyukan da alumma zasu dinga amfana ko bayan basa kan mulki ko sun mutu.
