Al’amarin ya faru ne a lokacin da ‘ƴan bindigan suka kai hari kan sansanin soji da ke Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala da yammacin ranar Litinin.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa a yayin harin kuma an kashe wasu daga cikin mayakan na Boko Haram da ba fadi yawansu ba.
Haka kuma wasu rahotanni na cewa kwamandan sojin da ya kai ɗauki ya taka nakiya da ta fashe, lamarin da ya janyo karin jikkata wasu da ma rasa rayuka.
Sansanin na Wulgo na bakin iyakar jamhuriyyar Kamaru, kuma yana ɗauke da sojin haɗaka na Najeriya da ƙasar ta Kamaru.
A baya-bayan dai ana ci gaba da samun ƙarin hare-haren daga ƙungiyar bayan an samu lafawarsu na wani lokaci.
