Gwamnatin tarayya ta ce alkalummanta da ta tattara sun nuna ana samun nasarar shawo kan matsalar tsaron da ta addabi sassan kasar da sama da kashi 80 cikin dari.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Birtaniya ta gargadi ‘yan kasarta da su kaurace wa yin balaguro a wasu sassan Najeriya bayan nuna damuwa kan karuwar hare-haren ta’addanci da satar mutane.
Jihohin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargadin sun hada da Borno da Yobe da Katsina da Zamfara da Adamawa da Gombe da kuma wasu jihohin na kudancin kasar nan.
Sai dai gwamnatin tarayya ta ce, alkalummanta na shekarar 2025 sun nuna ana samun saukin hare-haren ‘yan bindiga da kuma satar jama’a.
Gwamnatin ta kuma ƙara da cewa daga shekarar 2024 zuwa yanzu, ta samu nasarar gabatar da ƴanta’adda da ƴanbindiga sama 124 a kotu da aka yanke wa hukunci.
Da kuma kama jagororin kungiyar Ansaru da wasu da suka kai hari a asibitin Owo a 2022 da na Yelwata da sauransu da suke fuskantar shari’a.
