
Matatar mai ta Dangote ta ƙaryata rahoton da ake yadawa na cewa za ta iya rufe matatar mai na tsawon watanni biyu zuwa uku.
Mai magana da yawun rukunin kamfanin na Dangote, Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, rahoton “tsantsar ƙarya ce”maras tushe balle makama.
A wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, ya bayyana cewa, ‘‘akwai yiwuwar rufe sashen matatar man kamfanin wadda ke samar da ganga dubu dari 650 a kowace rana tsawon watanni biyu zuwa uku domin yin wasu gyare-gyare.
Rahoton ya kuma ƙara da cewa, matatar za ta yi ƙoƙarin komawa aikin tace mai na ganga 204,000 a kowace rana daga 20 ga watan Satumba.
Matatar mai ta Dangote, wadda ta soma sarrafa ɗanyen mai a watan Janairun 2024, ta sauƙaƙa harkokin mai na cikin gida tare da da kawo cikas ga harkar cinikayyar fitar da man fetur daga ƙasashen Turai zuwa yamma.