
Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7.
An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin Zamba da ke Abuja, yayin da ta ukun da ake zargin ma’aikaciyar jinya ce da ta tsere a yanzu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Henry Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis
Okoye ya ce, an kama waɗanda ake zargin ne a garin Owerri babban birnin jihar a ranar 14 ga watan Afrilu, biyo bayan wani samame da jami’an tsaro suka yi a lokacin da suke ƙoƙarin siyar da yaron kan kuɗi Naira miliyan 2.7
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin Zamba da ke Abuja, yayin da ta ukun da ake zargin ma’aikaciyar jinya ce wacce ta tsere.
“An kama mutanen ne biyu ne bayan ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin rundunar ’yan sandan Jihar Imo da hedikwatar ’yan sandan shiyya ta 7 da ke Abuja.
“An kuma miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na shiyyar Abuja, domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.