
Rahoton wani kwamiti da Gwamnatin jihar Filato da ta kafa don bincike game da hare-haren da ake kaiwa sassan jihar ya ce, maharan ba ‘yan asalin jihar bane sun fito ne daga maƙwabtan jihar da suka ƙunshi Kaduna da Bauchi da kuma Taraba.
Kwamitin wanda gwamnan jihar Kaleb Mutfwang ya kafa da nufin lalubo hanyoyin magance matsalolin da jihar ke fama da su na hare-hare masu alaƙa da ƙabilanci ko addini, na zuwa ne bayan tsanantar makamantan hare-haren a shekaru 2 da suka gabata.
Shugaban kwamitin Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas ya ce, bayan tattaunawa da mabanbantan ƙabilu da kuma ziyartar yankunan da hare-haren suka faru tare da tattara bayanai na kai tsaye daga waɗanda abin ya shafa, bayan zaman tattaunawa da su, game da yadda za a samar da zaman lafiya a jihar, sun gano cewa galibi maharan ba ƴan jihar ba ne.
A cewar Manjo Janar Rogers, sun gano cewa maharan da ke farmakar garuruwan galibi su kan shigo ne daga jihar Nasarawa ko Kaduna ko kuma Bauchi da Taraba.
Rahoton ya ce, wasu daga cikin ƴan bindigar da ke kai hare-haren tare da tilastawa al’ummar garin Quan’pan ficewa, sun kafa sansaninsu a ƙauyuka 2 na jihar Nasarawa da ke iyaka da Filaton.
Rahoton ya ce, ‘ƴanbindigar na shigo jihar ne ta garin Wamba da Lafia da Awe daga Nassarawa sannan daga iyakar Lere da Ƙaura da Sanga daga jihar Kaduna sannan sai waɗanda ke shigowa daga Bauchi ta iyakokin Toro da Tafawa Ɓalewa da Bagoro da Alƙaleri kana wasu daga iyakokin Ibi da Karim Lamiɗo daga Taraba.
Aƙalla garuruwa 420 ƴan bindigar suka kaiwa hare-hare wanda ya sabbaba asarar rayuka kusan dubu 12