
An tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Mokwa ta jihar Neja, wanda ya haifar da tare da ajalin kimanin mutane 50.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba da dare zuwa wayewar garin Alhamis.
Rahotann sun ce, babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin Najeriya da ta bi ta yankin ita ma ambaliyar ta yanke ta.
Duk da cewa, babu cikakkun bayanai a kan ambaliyar, amma mazauna yankin sun kiyasta cewa mutanen da suka rasa ransu za su kai 50.
Gidaje da sauran kadarori na miliyoyin nairori ne dai suka salwanta, yayin da wasu mazauna yankin kuma ke cewa adadin wadanda suka rasun ma zai iya wuce 50, sakamakon har yanzu akwai mata da kananan yara da dama da ba a san inda suke ba.
Aminiya ta rawaito cewa, mamakon ruwan saman da ya haifar da ambaliyar an kai da tsawon sa’o’i ana yin sa cikin dare inda ya cinye gidaje yayin da mutane suke tsaka da barci.
Wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Usman ya ce, an tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwa, amma har yanzu akwai wadanda ba a kai ga gano su ba, musamman a wuraren da gidajen suka nitse baki daya.
Daraktan Yada Labarai na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dakta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar ambaliyar
Shugaban ya kuma ce, har yanzu hukumar na kan aikin tattara bayanai da alkaluma kafin ta kai ga sanar da abin da ta gano.