Majalisar wakilai ta yi watsi da bukatar da aka gabatar mana na kirkirar sababbin jihohi a kasar nan har guda 36.
Wanann na zuwa ne biyo bayan yadda bukatar hakan ta gaza cika sharuddan da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada domin tabbatuwar hakan.
Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai kula da yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima, ya bayyana hakan ne a yau Juma’a.
Inda ya ce bukatar da aka gabatarwa majalisar tun a ranar 6 ga wannan wata na Fabrairu ta gaza cika sharukan dake karkashin sashi na 8 na kundin tsarin mulkin wannan kasa dake Magana akan kirkirar sabuwar jiha.
To sai dai Kalu ya ce har yanzu lokaci bai kure ba domin kuwa idan aka cika kaidar data kamata za a iya sake gabatar da kudurin gaban majalisar daga yanzu zuwa abun da bai wuce ranar 5 ga watan Mayu.
Ya kara da cewa yanzu haka kwamitin majalisar mai kula da batun kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin na kasa yanzu haka yana da kudurori har 151 da yake fatan dubasu, wadanda suka jibanci bangarori da dama ciki har da batun yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi da sauransu.
