Majalisar Wakilai ta kafa wani kwamitin bincike na musamman domin duba zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID) na bayar da tallafi ga ƙungiyar Boko Haram.
Wannan mataki ya biyo bayan buƙatar gaggawa da ɗan majalisa Inuwa Garba ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Garba ya nuna damuwa kan furucin ɗan majalisar dokokin Amurka Scott Perry, wanda a kwanakin baya ya zargi hukumar da bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda tallafi ciki har da Boko Haram.
A cewarsa, ƙungiyar Boko Haram ta haddasa babbar matsalar tsaro a Najeriya tsawon sama da shekaru goma, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da asarar dukiya mai tarin yawa.
Bayan tattaunawa a majalisar, Kakakinta ya kafa kwamitin bincike na musamman domin nazarin batun.
Ana sa ran kwamitin zai kammala bincikensa tare da gabatar da rahoto cikin makonni biyu masu zuwa.
