
Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da sabbin sansanonin horar da dalibai masu yiwa kasa hidima (NYSC).
Majalisar ta kuma bukaci gwamnati ta inganta wadanda ake da su domin bawa daliban damar daukar horo a sansanin yadda yakamata.
Dan Majalisar Garba Muhammad ne ya gabatar da bukatar hakan a zaman majalsar na Alhamis, Kudurin kuma ya samu amincewar mambobin karkashin shugaban ta Tajuddeen Abbas.
Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta hada kai da gwamnatocin jihohi wajen samar da karin sansanonin da daliban ake turo wa daga manyan makarantun kasar nan don aikin yi wa kasa hidima.
A baya dai hukumar kula da dalibai masu yiwa kasa hidima NYSC ta koka kan rashin ingancin wasu sansanonin daliban tare da bukatar gwamnati ta inganta su.