Majalisar dokoki ta Iran ta amince da wani ƙudiri da ke neman yanke hulda da hukumar kula da nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya saboda hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa tashoshinta.
Matakin zai ta’azzara rashin jituwa tsakanin Iran da hukumar mai suna International Atomic Energy Agency (IAEA) wanda kuma zai iya zama giɓi a ɓangaren sa ido kan shirin Iran na nukiliya.
Ƙudirin da aka amince da shi a ranar Laraba, zai hana sa ido, da ayyukan tattara bayanai, da kuma bayar da rahoto da ma’aikatan IAEA ke yi a Iran.
Duk da cewa sai majalisar shura ta Iran ta amince da ƙudirin kafin ya zama doka, hakan na ƙara fito da matsayin Iran game da shirinta na nukiliya.
Ɗanmajalisa Ebrahim Rezaei, mai magana da kwamatin majalisar, ya ce an ɗauki matakin ne da zimmar jaddada ‘yancin Iran kan abin da ya kira hukumar da aka siyasantar da ita.
