Kwamitin kula da baitul mali na Majalisar Dokokin jihar Kano ya koka da rashin bibiyar yadda gwamnatin jihar ta ke aiwatar da kasafin kudinta har na tsawon shekaru 7.
Haka ma rabon da bibiyar yadda kananan hukumomin jihar suke kashe nasu kudadensu shekaru 13 kenan. Inji kwamitin.
Shugaban kwamitin kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Fagge, Tukur Muhammad ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki da ofishin mai binciken kudi na gwamnatin Kano a ranar Alhamis.
Ya kuma ce, kwamitin yana aiki tukuru domin farfado da ayyukansa.
A jawabinsa a taron Mai Binciken Kudi na jihar, Isma’ila Musa, ya ce wannan na cikin ayyukan da doka ta basu damar gabatarwa, kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta ce domin amfanin al’ummar jihar Kano.