
Majalisar Dattawa ta shiga tsakani don warware rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU), a wani yunƙuri na kawo ƙarshen yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da malaman jami’ar ke yi.
A sakamakon haka, kwamitocin Majalisar Dattawa kan Kwadago da kuma Ilimi mai zurfi za su gana da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da Sakatare-Janar na hukumar Jami’o’i ta ƙasa (NUC), Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu, a ranar Talata mai zuwa.
Wannan ganawa ta biyo bayan taron da kwamitocin suka gudanar da shugabannin ASUU a majalisar a ranar Juma’a, inda suka tattauna kan hanyoyin da za su bi don magance matsalolin da suka janyo yajin aikin. Shugaban kwamitin kan Ilimi mai zurfi da TETFund, Sanata Muntari Dandutse. ya bayyana wa manema labarai cewa sun saurari ƙorafe-ƙorafen ASUU kuma za su gabatar da su ga hukumomin da abin ya shafa.
A nasa jawabin kafin taron sirrin, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Christopher Piwuna, ya ce buƙatar ƙungiyar ita ce gwamnati ta inganta kuɗaɗen gudanar da jami’o’i kamar yadda aka amince a yarjejeniyoyin baya. Ya bayyana cewa zuba jari mai ɗorewa a fannin ilimi ne kaɗai zai kawo ƙarshen yajin aiki da kuma ƙara matsayi ga jami’o’in Nijeriya a matakin duniya.
Farfesa Piwuna ya ce ASUU ta shafe shekaru takwas tana tattaunawa da gwamnati ba tare da sakamako mai gamsarwa ba, inda ya ambaci rahoton kwamitin Yayale Ahmed na Disamba 2024 da aka yi watsi da shi har sai bayan da yajin aikin ya fara. Ya kuma bayyana cewa daga cikin Naira biliyan 150 da majalisar ta amince da su domin jami’o’i, Naira biliyan 50 kawai aka saki, kuma tana maƙale a ma’aikatar ilimi. Ya gargaɗi gwamnati da kada ta karkatar da kuɗin zuwa wasu cibiyoyi kamar kwalejoji da polytechnic, domin an ware su ne musamman don jami’o’i.