
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sha alwashin gudanar da bincike kan zargin da wasu manoma suka gabatar kan shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Yusha’u, kuma shugabar kungiyoyin kananan hukumomi (ALGON) na jihar.
Zargin ya shafi kwace gonaki da ke Dajin Gurfa da ke cikin karamar hukumar Tudun Wada, wanda ya haifar da ƙorafi daga manoman da abin ya shafa.
Majalisar ta bayyana aniyar gudanar da bincike mai zurfi domin tantance gaskiyar lamarin da kuma nemo mafita mai dorewa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Lawan Hussaini Cediya Ƴan Gurasa, ne ya bayyana haka bayan amsa gayyatar wata kungiya mai zaman kanta da ke kare haƙƙin ɗan’adam da tabbatar da daidaito a cikin al’umma.
Kungiyar ta shigar da ƙorafi a madadin manoman da lamarin ya shafa.
Shugaban kungiyar, Sa’id Bin Usman, ya bayyana cewa akwai tarin ƙorafe-ƙorafe da ke tattare da rikicin mallakar gonaki a yankin, inda ya zargi shugabancin karamar hukumar da hannu a cikin batun kwace filayen noma daga hannun manoman da suka dade suna amfani da su.
“Akwai matukar buƙatar a duba wannan lamari domin tabbatar da adalci da kare haƙƙin waɗanda aka zalunta,” in ji Sa’id.
Wasu daga cikin manoman da suka shigar da ƙorafin sun bayyana cewa gonakin da ake magana a kai su ne hanyarsu ta rayuwa, kuma sun dade suna amfani da su kafin kwace su ba tare da wani sahihin bayani ko diyya ba.
Majalisar ta tabbatar da cewa za ta yi duba na gaskiya da rikon amana, tare da sauraron bangarorin da abin ya shafa, domin ganin an samu adalci da bin doka da oda.