Majalisar dattijai na shirin zartar da sabbin dokokin haraji mai cike da cece-ku-ce duk da nuna kin jinin kudurin sauya-sauyen daga arewa.
Majalisar dattijai ta yi ta yi zaman karatun dokoki harajin na biyu a ranar Alhamis.
A zaman majalisar na ranar Laraba ne Sanata Ali Ndume ya jagoranci ficewar wasu ‘yan uwansa sanatoci daga zauren majalisar don nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira kutse na wasu da aka kira su yi musu jawabi kan tattara haraji.
Bayan sa-in-sa da mataimakin majailisar Barau Jibrin da ya jagoranci zaman majalisar kan karya ka’idar.
Sanatocin na arewa sun ce sun yi hakan ne don rashin amincewarsu da karya ka’idar da ake bi na kiran wasu daga waje da kuma kin jininsu ga dokar.
Daukacin gwamnonin arewa da sarakuna da kuma datttawan yankin duk sun nuna rashin yardarsu ga samar da dokar da suka za ta shafi tattalin arzikin yankin baki daya.