Daga ketare, Ma’aikatar tsaron kasar Benin da takwararta ta Amurka sun shirya taron karawa juna sani na ƙasa da ƙasa a birnin Kwatanu na Jamhuriyar Benin, wanda a gefe daya kuma taron zai yi duba a kan tasirin mutunta dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa.
Rahotanni daga ƙasar ta Benin na nuni da cewa kusan ƙasashe 30 na Afirka ne suka turo da wakilcin kwamandojin rundunan soji da masu ba su shawara kan harkokin shari’a.
Manufar horon ita ce ƙarawa juna sani a fannin da ya jibanci aikin doka daga jami’an tsaro da nufin samar da daidaito tsakanin tasirin aikin soja da mutunta ka’idojin jin kai.
Wani babban jami’i daga Congo Brazzaville, Juste Ndanou Mauriac ya bayyana cewa barazanar da yawancin ƙasashen Afirka ke fama da ita, tana da alaka da tsaro, inda ‘yan ta’adda ke amfani da damar su wajen azabtar da mutanen da suke tsare da su ko suke afkawa a hare-haren da suke kaiwa, wanda ke dagula bin dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa.
Wannan dai ita ce ka’ida ta farko da aka tsara, kuma dole ne mu san yadda za mu dace da wannan ƙalubale na yaƙin da yan ta’adda.
