Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta kaddamar da aikin kwashe shara a cikin birnin Kano.
Sabon kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim ne ya kaddamar da shirin a safiyar litinin din nan, a kasuwar Kantin Kwari.
Kwamishinan ya ce an dorawa hukumar kwashe shara REMASAB alhakin kwashe duk sharar dake titina, kasuwanni, tashoshin mota, asibitoci, makarantu, hukumomi, unguwanni tare da lungu da sako na jahar Kano.