Ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare tsare ta jihar Kano ta ce tana fatan cimma nasarar manufofinta da ya sanya ta ke gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan kasafin kuɗi.
Kwamishinan ma’aikatar Musa Sulaiman Shanono, ne ya bayyana haka yayin taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki a sha’anin kasafin kudi a jihar Kaduna.
Kwamishinan yace akwai tarin ƙalubale da suke fuskanta a bangaren kasafin kudi musamman daga wasu ma’aikatu.
A nasa ɓangaren mataimakin kakakin majalisar dokokin Kano Muhammad Bello Ɓutu-Ɓutu, yace majlisar ta kafa kwamiti domin fito da hanyoyin magance matsalar jinkiri da ake samu wajen gabatar da bayanan hukumomin gwamnati.
Taron ya samu halartar shugabannin manyan ma’aikatun jihar Kano da ƙananan hukumomi da ƙungiyoyin fararen hula.
