
Ma’aikatan Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIMET) sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, sakamakon saba yarjejeniyar da ke tsakaninsu da shugabancin hukumar.
Yajin aikin ya biyo bayan gazawar NIMET wajen aiwatar da matakan da aka cimma a yarjejeniya tun farkon wannan shekara.
A wata sanarwa da kungiyoyin ma’aikata suka fitar, sun zargi hukumar da kin cika alkawurukan da suka kulla ta kuma yin watsi da bukatun ma’aikata.
“Mun shiga wannan yajin aikin ne domin kare martabar ma’aikaci da kuma tabbatar da cewa ana aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, musamman wadanda suka shafi walwala da jin dadin ma’aikata,” in ji wata sanarwa daga kungiyar.
Kungiyoyin sun bayyana cewa tun watan Janairu na shekarar 2025 aka kulla yarjejeniya da shugabancin NIMET, amma har yanzu babu wani abin a zo a gani da ke nuna an dauki matakin aiwatar da ita.
Sun kuma jaddada cewa yajin aikin da suka taba yi a baya bai haifar da gagarumin sauyi ba, dalilin da yasa suka dauki matakin komawa yajin aikin na sai baba ta gani.
Sanarwar ta kuma bukaci dukkan ma’aikatan da ke aiki a sashin sufurin jiragen sama a fadin kasar nan da su mara wa yajin aikin baya, domin a samu nasarar tilasta aiwatar da bukatun da suka dade suna jira.