
Wannan na zuwa ne bayan cimma yarjejeniyar kungiyoyin ma’aikatan hukumar da ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo.
Sakataren Kungiyar Ma’aikatan Sufurin Sama (NUATE), Kwamarad Aba Ocheme ya tabbatar da janye yajin aikin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis da dare.
Sai dai sanarwar ta ce, ta dakatar da yajin aikin ne zuwa ranar 13 ga watan Mayun shekarar 2025, kafin daukar mataki na gaba.
Ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin ne a Sakamakon kin aiwayar da Karin albashin da suka cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya.
Wanda hakan ya kawo cikas ga sauka da kuma tashin jiragen sama a manyan tasoshin jiragen sama na kasa.