Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da biyan ƙarin albashin Naira 5,000 ga ma’aikatan ƙananan hukumomi da Hukumar Ilimi ta Ƙananan Hukumomin jihar, wanda zai fara aiki daga albashin watan Yunin da muke ciki.
Wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar Ahmed Abdullahi ya sanyawa hannu ta ce, an cimma matsayar ne a wani taro na musamman da aka gudanar tsakanin Shugaban Ma’aikatan da wakilan ƙungiyoyin kwadago da wasu manyan jami’an gwamnati a jihar.
Sai dai duk da ƙarin albashin, wani bincike ya gano cewa har yanzu ma’aikatan ƙananan hukumomi 11 na jihar ba su fara cin gajiyar ƙarin mafi karancin albashi da aka yi ba.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Dokta Manassah Jatau, tare da shugabannin ƙungiyar ƙwadago reshen jihar, Yusuf Bello, sun amince cewa idan kuɗaɗen shiga sun ƙaru, za’a fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70,000 ga ma’aikata.
