Kungiyar ‘Yan Jarida masu dauko labari daga Kotu ta Najeriya (NCJC), ta taya al’ummar Musulmi murnar bikin babbar sallah (Eid-ul-Adha).
Sakataren Kungiyar na jihar Kano, Kwamared Abubakar Haruna Galadanchi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa PremierRadio, inda Kungiyar ta yaba wa al’ummar jihar a bisa nasarar gudanar da bukukuwan Sallar cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ƙungiyar ta kuma yaba wa mutanen Kano, a bisa juriya, hadin kai da kishin zaman lafiya da suka nuna wanda ya sanya bukukuwan bana suka kasance na musamman.
A cewar Galadanchi, “Abu mai kayatarwa shi ne yadda bukukuwan suka gudana ba tare da rahoton wani rikici ko matsala ta tsaro ba a fadin jihar ba, duk da cewa an fuskanci barazana a wasu wurare, sai dai bajintar jami’an tsaro da hadin kai daga jama’a ya tabbatar da ingancin ayyukan hukumomin tsaro a jihar”.
“Adan haka muna jinjinawa kokarin jami’an tsaro, musamman hukumar tsaron farin kaya (DSS), Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, rundunar tsaro ta Civil Defence da sauran hukumomin tsaron da ke aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya da doka a jihar”.
Ƙungiyar ta kuma jinjinawa masu rike da sarautun gargajiya, musamman Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, la’akari da yadda suka taka rawar gani wajen jagoranci da kuma wayar da kai al’umma akan muhimmancin zaman lafiya wanda hakan ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
A ƙarshe ƙungiyar ta yi addu’ar Allah ya kara tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano da Najeriya baki daya.
