Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta.
Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da mako guda da irin wannan ibtila’i ya faru, domin a kwanaki shida da suka gabata, mutane huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale makamancin wannan a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar.
waɗanda abin ya rutsa da su sun gaggauta shiga kwale-kwalen ne a ƙoƙarin tsere wa ‘yan bindigar da suka hango sun yi kwanton ɓauna.
Kazalika, wani mazaunin ya ce an shiga zaman ɗar-ɗar ne lokacin da suka hangi ‘yan bindigar na tunkaro su, lamarin da ya sa suka yi gaggawar shiga kwale-kwalen da ta kife a tsakiyar ruwa saboda an yi masa lodin da ya fi ƙarfinsa.
