
Wata Babban Kotun ta aike da wani dan Tiktok zuwa gidan yari a bisa zargin cin zarafin wasu ‘yan Kannywood.
Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Fina-Finai ta Kasa (MOPPAN) ce ta kai karar Ahmad Pasali kan zargin kazafi da bata sunan wasu ‘yan masana’antar Kannywood a gabanta.
Kotun dake zamanta a kasuwar Nama a garin Jos, Jihar Filato, ta aike da matashin dan Tik tok din ne a Litinin 3 ga Maris bayan gaza cike ka’idojin belinsa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Kungiyar na kasa Ibrahim Amarawa ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce, bayan karanto masa tuhume-tuhumen da ake yi masa a yayin zaman Kotun, Pasali ya musanta laifin, yayin da lauyansa ya nemi kotu ta ba da belinsa.
Alkalin kotun Justice Thomas Nakowa, ya gindaya sharuddan beli da suka hada da ajiye Naira 250,000, da gabatar da mai tsaya masa da ke da gida a garin Jos da gabatar da takardun gidansa da kuma amincewar dan kungiyara MOPPAN zai tsaya masa.
Rashin cika sharuddan ta sa aika aike da shi gidan gyaran hali har zuwa 5 ga Afrilu, lokacin da za a ci gaba da sauraron shari’ar.
