Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa (NARD) reshen Abuja, ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Talata, a matsayin martani ga korar jami’an lafiya 127 da Hukumar Kula da Ayyukan Gwamnati Ta Birnin Tarayya (FCTA) ta yi.
Shugaban kungiyar, Dakta George Ebong ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai bayan taron gaggawa da aka gudanar a yammacin Litinin a Abuja.
Shugaban ya ce, matakin ya zama dole domin kare hakkokin likitocin da abin ya shafa.
“A ranar Jumu’a ne FCTA ta sallami jami’an lafiya 127 ba tare da bin ka’ida ba. Wannan abu ya sabawa dokokin aiki kuma yana barazana ga tsarin kiwon lafiya na Abuja. Muna bukatar a dawo da su bakin aiki tare da biyan su albashin watan Afrilu,” in ji Dakta Ebong.
Shugaban ya kuma bukaci shugaban Hukumar Kula Da Aikin Gwamnati Ta Abuja, Emeka Ezeh, da ya sauka daga mukaminsa, yana mai zargin sa da rashin adalci da gazawa wajen tafiyar da al’amuran ma’aikatar.
Haka zalika shugaban Kungiyar NARD ya yi gargaɗin cewa idan Ministan Abuja, Nyesom Wike, bai dauki mataki don warware lamarin ba, kungiyar za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani bayan kammala na kwanaki uku.
Yajin aikin ya haifar da damuwa a cibiyoyin kiwon lafiya a Abuja, inda ake fargabar karin cunkoso da tabarbarewar ayyukan jinya idan ba a warware rikicin cikin lokaci ba.
