
Likitoci a kasar Sudan sun zargi dakarun RSF da ke yaƙi da sojojin ƙasar da kashe fararen hula guda 13 a Arewacin Dafur, a daidai lokacin da yaƙi ke ƙazancewa a yankin El Fasher, wanda shi kaɗai ne ya rage a hannun sojojin ƙasar a cikin manyan biranen Dafur a yanzu.
A wata sanarwa da gamayyar likitocin suka fitar, sun ce daga cikin waɗanda mayaƙan suka kashe akwai ƙananan yara biyar.
Lamarin ya auku ne a wata babbar hanyar da ta raba birnin El Fasher da Tawila, inda likitocin suka ce, “yunƙurin kisan ƙare dangi ne.
Andaɗe ana zargin RSF da kai hari kan garuruwan da ba Larabawa ba ne a Dafur, duk da cewa sun sha musanta zargin.
Ana dai ci gaba d gwabza yaƙi tsakanin RSF da sojojin Sudan a ƙasar tun bayan da yaƙin basasa ya ɓarke a ƙasar.