Hukumomin Lebanon sun saki Hannibal Gaddafi, ƙaramin ɗan tsohon shugaban Libya, Marigayi Muammar Gaddafi, bayan kusan shekara 10 a tsare ba tare da shari’a ba.
A shekarar 2015 ne hukumomin Lebanon suka tsare Hannibal Gaddafi, bayan da suka zarge shi da ɓoye bayanai kan wani fitaccen malamin shi’a da ya ɓace a Libya a 1978, a lokacin Hannibal na shekara biyu kawai a duniya.
An sake shi ne a ranar 10-11 ga Nuwamba 2025, bayan biyan ragin beli na dalar Amurka 900,000.
An tsare Hanbali ne a watan Disamba na 2015 bayan da hukumomin Labanon suka zarge shi da boye bayanai game da bacewar sanannen malamin Shi’a na Labanon, Musa al-Sadr, da abokan tafiyarsa a 1978, lokacin ziyarar da suka kai kasar Libya.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama, ciki har da Human Rights Watch sun yi tir da tsare shi da aka yi, suna kiran zarge-zargen “na bogi” saboda Gaddafi yana dan shekara biyu kacal a lokacin da lamarin ya faru kuma bashi da wani mukami na gwamnati a lokacin da ya girma.
Da farko wani alkali ya sanya belinsa a kan dalar Amurka miliyan 11, amma daga baya aka rage kudin zuwa kusan dalar Amurka 900,000 bayan kungiyar lauyoyinsa suka daukaka kara.
Hukumomin Labanon sun kuma dage takunkumin tafiye-tafiye, kuma ana sa ran zai bar kasar Labanon zuwa wani wuri “na sirri”.
Sakin nasa ya biyo bayan ziyarar da wata tawagar gwamnatin Libya ta kai Beirut, kuma gwamnatin hadin kan kasa (GNU) da ke Tripoli ta nuna godiya ga hadin gwiwar da aka yi da jami’an Labanon. Rahotanni sun ce hukumomin Afirka ta Kudu sun amince su karbi bakuncinsa.
