Wani lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam ya kai karar Ministan Abuja bisa kamen mabarata a Babban Birnin na Tarayya.
Barista Abba Hikima, dan asalin jihar Kano, ya shigar da ƙarar ne a bisa cewa kamen ya saɓawa tsarin mulkin Nijeriya, kuma hakan take hakkinsu ne.
Lauyan ya kuma zargi hukumomin birnin da cin zarafin masu karamin karfi da suka hada da almajirai da kananan ‘yan kasuwa da kuma wadanda ba su da wurin kwana.
Ya kuma nemi a biya su Naira Miliyan Dari Biyar a matsayin ladan wahalar da su, sannan gwamnati ta nemi gafarar su a bainar jama.
Kwanan baya ne Ministan Abuja ya ƙaddamar da kama mabarata da kuma wadanda ta kira zauna gari banza a wani mataki na tsabtace birnin.
Ministan ya ce, sun cika titunan birnin, sun kuma zama barazana ga tsaro da zubar da mutuncin kasa a idon baƙi, a cewar Wike.
Sauran wadanda ake tuhuma a karar da lauyan ya shigar sun hada da Babban sufeton ‘yansanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS da Babban Kwamandan Rundunar Tsaro Sibil Difense da kuma ministan shari’a.
Ranar Laraba ne ake sa ran Babbar Kotun Tarayya za ta sa ranar fara sauraron ƙarar.