
Daga Ibrahim Hassan Hausawa
Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi na II ya yi kira da a dau kwakwarren mataki kan batun kisan ‘yan jihar Kano a Edo.
Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da hudubar sallar idi a masallacin idi na cikin gari dake Kofar Mata a ranar Lahadi.
“Yadda wasu daga cikin mahukunta suka magantu kan batun kisan abin a yaba ne, amma akwai bukatar duk mai ruwa da tsaki ya tabbatar da an dauki hukuncin ladabtarwa kan duk mai a hannu cikin aika-aikar” in ji shi.
Sarkin na Kano ya kara da jan hankalin matasa musamman anan Kano akan su gujewa daukar fansa kan abokan zamansu, yana mai cewa ramuwar gayya haramun ce a addini.
Baban Limamin Kano Farfesa Sani Zaharadden ne ya jagoranci sallar da ta samu halartar hikimai da kwamishinonin gwamnatin Kano da kuma daruruwan jama’a