
Gamayyar Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam a Kano ta bukaci a samar da tsarin daukar nauyin rayuwar iyalan matafiya 16 da aka kashe a jihar Edo.
Shehu Abdullahi, babban jami’in hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta kasa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Kano.
“Kundin tsarin mulki na Najeriya ya tanadi biyan diyyar rayuka. Bayan haka haka ya zama wajibi a dauki nauyin rayuwa da ilimin ‘ya’yan da suka bari, da sauran bukatunsu.” In ji shi.
Gamayyar Kungiyoyin ta kuma bukaci gwamnan jihar Edo da na Kano su tabbatar da aiwatar da tsarukan da suka tsara kan wannan lamarin domin tabbatar da adalci da kare hakkin dan adam.
Kungiyoyin sun yi alkawarin ci gaba da bibiyar lamarin domin tabbatar da cewa an samu adalci da kuma kaucewa irin wannan mummunan abu a nan gaba.