Rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja, ta musanta rahotannin da ke cewa an yi yunƙurin kashe jami’in sojan ruwa, Laftanar Ahmed Yerima.
Kakakin Rundunar ‘Yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar, a ranar Litinin.
“An samu rahoton faruwar lamarin ba, kuma babu wata shaida da ta nuna an yi yunƙurin kisan jami’in a birnin.
“Rundunar tana kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan wajen yada labaran da ba su da tushe, domin kauce wa tayar da hankalin jama’a.
A ranar Lahadin nan ne jaridar Vangaurd ta rawaito cewa, wasu da ba a san ko su wanene ba, a cikin motocin Hilux biyu da babu lamba, sun bi diddigin jami’in a hanyan Kubwa zuwa titin Gado Nasco, da niyyar halaka shi.
Jaridar ta bayyan wata majiya a rundunar sojin kasa a matsayin madogara
