Gwamanan kano Abba Kabir yusuf Ya jajanta rasuwar mamacin yayin zaman majalisar zartaswa karo na 33 a fadar gwamnatin Kano na yau Asabar.
Abba Kabir Yusuf, ya yi addu’ar Allah yajikansa tare da baiwa iyalansa hakurin jure rashin sa.
- Mu Da Kwankwaso Mutu Ka Raba – Gwamnan Kano
- Tarihi: Yau shekara 100 da jirgin sama na farko a Najeriya ya sauka a Kano
Ya kuma jagoranci addu’a yayin zaman majalisar zartaswar ga Dr Muhammad Hassan Lawan Koguna da wanda ya rasu a daren ranar Juma’a wayewar Asabar
Dr Koguna ya rasu bayan fama da doguwar jinya a Asibitin Nizemia dake Abuja.
