
Tsohon gwamnan ya kuma yi kira da a gudanar da binciken kwakwafa don gano da kuma hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wannan kiran ne a shafinsa na X a ranar Juma’a a inda ya kira kisan da tsagawaron rashin imani da keta hadi.
“Kowa a kasar nan yana da ikon zirga-zirga zuwa inda yake so ya kuma zauna inda ya ke so ba tare da tsangwama ba.
“Don haka ina kira ga jami’an tsaro da hakkin yake a kan su da gudanar da binciken yadda lamarain ya faru tare da zakulo wadanda suka aikata kisan da kuma hukunta su.” In ji shi.
A ranar Juma’a ne aka wayi gari da hotuna da kuma bidiyo na wasu mafarauta 16 ‘yan arewa daga garin Fatakwal kan hanyarsu ta zuwa arewa, wasu ‘yan banga a garia Udune Efadion a jihar Edo suka tare motarsu.
Bayan gano tarin bindigogi da sauran kayan farauta suka fito da su daya bayan-daya suka sassara su tare da cinna musu da kone su kurmus, a cewar rahotanni.
Wanda haka ya janyo cece-kuce da Allah wadai a kafafen sada zumunta kan hujjar mutanen garin na daukar wannan danyen hukunci.