Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (NNPP) a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana jin daɗinsa bisa gaggawar cafke mutanen da ake zargi da hannu a mummunan kisan da aka yi wa
Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a Unguwar Dorayi Chiranchi, Jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Kwankwaso ya bayyana kisan a matsayin mai ban tsoro, da taɓa zuciya
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar Dorayi Chiranchi da kuma daukacin al’ummar Jihar Kano, yana mai cewa lamarin ya jefa jihar cikin alhini da baƙin ciki.
Kwankwaso ya yabawa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano kan yadda suka nuna ƙwarewa ta hanyar bincike da bayanan sirri, wanda hakan ya kai ga cafke waɗanda ake zargi cikin ’yan awanni bayan faruwar laifin.
Haka kuma, ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su kasance masu tsayuwar daka da sa ido, tare da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin jama’a domin daƙile tashin hankali da inganta tsaro.
